Wasu Gungun 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyar (5) Tare da Sace 27 a Kaduna


Rahotanni daga jihar Kaduna sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kai hare-hare a ƙananan hukumomin Giwa da Kubau, inda su ka kashe mutane biyar, ciki har da jami'an hukumar sintiri ta Kaduna, Kaduna State Vigilance Service (KadVS), tare da yin garkuwa da wasu 27.

Jaridar Tribune ta rawaito cewa a ƙaramar hukumar Giwa, ’yan bindigan sun kashe mutane biyu a garuruwan Tunburku yayin da suka yi garkuwa da wasu a ƙauyen Tudun Amada sannan kuma a Kubau suka kashe wasu daga cikin jami’an KadVS.

Jami’in hulɗa da jama’a na KadVS, Yunusa Shehu, ne ya tabbatar da hare-haren a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Ya ce ’yan bindigan sun kai hari a Tunburku da Tudun Amada da sanyin safiyar Litinin.

Wanda a harin aka kashe Alhaji Surajo da Alhaji Ado a Tunburku, yayin da aka sace mutane 26 a Tudun Amada. Wani mazaunin yankin mai suna Ayyuba Usman kuma ya samu raunuka.

Yayin da a wani hari da ya faru a Kubau kuma, ’yan bindigan sun kashe jami’an KadVS uku yayin da suke gudanar da aikin sintiri a yankin Zaria-Pambegua.

Jami’an da aka kashe sun haɗa da Ɗallami Ɗantani, mataimakin kwamandan KadVS a Kubau, da kuma Abdullahi Hamisu da Zakariyya Musa.

Rahotanni sun ce jami’an sun yi musayar wuta da ’yan bindigan yayin da suke bin wata mota da suka yi zargin tana ɗauke da waɗanda ake zargi. An kashe jami’an uku kafin maharan su tsere zuwa wajen Zariya.

Haka kuma, ’yan bindigan sun yi garkuwa da Sanusi, ƙanin ɗan majalisar dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Kubau, Shehu Pambegua. An sace shi daga gidansa da misalin ƙarfe 10 na dare ranar Litinin.

Kwamandan KadVS na jihar, CP Ali Audu (mai ritaya), ya jajanta wa iyalan jami’an da aka kashe, tare da yabawa jami’an bisa jajircewarsu wajen kare al’umma.

Ya ce an ƙara tsaurara matakan tsaro a Pambegua da sauran ƙauyukan da ke kewaye, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin gano inda mutanen da aka sace suke tare da kamo waɗanda suka aikata hare-haren.

Post a Comment

Previous Post Next Post