Wasu rahotanni daga Amurka sun ruwaito cewa Ma’aikatar tsaron ƙasar, Pentagon na shirin duba yiwuwar kai wani sabon hari kan Iran a cikin kwanaki masu zuwa.
Shafin labarai na Axios, ya ambatoo jami’an Amurka, na cewa a kwanakin baya-bayan nan Pentagon ta umarci CENTCOM, wato rundunar sojin Amurka mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya, ta kammala shirye-shiryenta domin yiwuwar sake fara manyan hare-haren soja kan Iran.Ita ma mujallar The Atlantic, a wani rahoto na musamman da ta wallafa tare da ambato wasu jami’an Amurka biyu, ta ce Fadar White House ta buƙaci Pentagon ta tsara zaɓuɓɓukan kai hare-hare kan wurare a Iran da za a iya aiwatarwa kafin zaɓukan tsakiyar wa’adin mulki na Amurka.
A cewar The Atlantic, shugaban Amurka Donald Trump na da muradin ganin an rage farashin man fetur tare da samun gagarumin ci gaba a rikicin da Iran kafin gudanar da zaɓen.
Sai dai Axios ta ce umarnin da Pentagon ta bayar bai ƙayyade takamaiman ranar da za a fara hare-haren ba, kuma har yanzu Donald Trump bai yanke hukunci na ƙarshe ba kan lamarin.
Duk da haka, majiyoyin Amurka da Isra’ila sun shaida wa Axios cewa ana iya ɗaukar matakin kafin zaɓukan tsakiyar wa’adin mulkin Amurka, watakila ma kafin zaɓukan Isra’ila da ake gudanarwa mako guda kafin na Amurka.
Ana sa ran gudanar da zaɓukan tsakiyar wa’adin mulkin Amurka cikin ƙasa da wata guda, a ranar 3 ga watan Nuwamba.
Axios ta kuma ruwaito, wasu majiyoyin da ta bayyana a matsayin masu cikakken bayani kan lamarin, na cewa idan aka sake fara manyan hare-hare kan Iran, akwai yiwuwar su haɗa da kai hare-hare ta sama kan cibiyoyin makamashi, manyan kayayyakin more rayuwa da kuma wuraren da ke da alaƙa da shirin nukiliyar ƙasar.