Ana sa ran tattalin arzikin Najeriya zai riƙa haɓaka da aƙalla kashi 4.4 cikin ɗari a shekara daga yanzu zuwa shekarar 2028.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto na Reuters ta kalato daga bankin duniya, inda ta ƙara da cewa hauhawar farashi kuma za ta ci gaba da raguwa a hankali, sannan kuma talauci ya fara sauƙaƙa.Sai dai rahoton ya ce wannan zai faru ne matuƙar gwamnati ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki tare da inganta ayyukan yi wa jama'a hidima, a cewar Bankin Duniya a ranar Alhamis.