An Kai Hari Filin Riyadh na Saudiyya

Harin ya yi sanadin mutuwar mutane uku yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon hare-hare biyu da aka kai kan filin jiragen saman Sarki Khalid da ke Riyadh a ranar Alhamis, kamar yadda Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA) ta sanar a ranar Juma'a.

Jirgi
Jaridar Saudi Gazzet ta ambato hukumar na cewa harin farko ya yi wa wasu sassa na filin jirgin saman illa, yayin da na biyu ya auka wa wani jirgin sama na kamfanin Saudia.

A cikin wata sanarwa, GACA ta ce tawagogin kai ɗaukin gaggawa da sauran hukumomin da abin ya shafa sun yi gaggawar mayar da martani ga hare-haren biyu bisa tanade-tanaden da aka shimfiɗa na gaggawa da kuma tsare-tsaren ko-ta-kwana.

Hukumar ta ce hare-haren sun jikkata wasu ƴan ƙasar da mazauna ƙasar na ƙabilu daban-daban.

Tuni ƙungiyar ƴantawaywen Houthi ta ɗauki alhakin kai harin

GACA ta ce tana ci gaba da tantance irin asarar da aka yi tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro masu ruwa da tsaki, tare da ɗaukar duk matakan da suka dace domin tabbatar da lafiyar fasinjoji da ma'aikatan filin jirgin sama, da kuma kare tsarin sufurin jiragen sama na farar hula na Saudiyya.

Hukumar ta ce tuni aka koma zirga-zirga a filin jirgin.

Post a Comment

Previous Post Next Post