Kasashen Nijar da Rasha Sun Ƙara Ƙarfafa Haɗin Gwiwa a Fannin Makamashi da Noma da Kuma Sufuri

Shugaban Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, ya karɓi wata babbar tawagar Rasha ƙarƙashin jagorancin Ministan Makamashin ƙasar, Sergei Tsivilev, a fadar shugaban ƙasa da ke Yamai.

Ganawar ta biyo bayan taron farko na kwamitin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatocin Nijar da Rasha, wanda ya tattauna kan faɗaɗa hulɗar ƙasashen biyu a fannonin makamashi da noma da kuma sufuri da kiwon lafiya gami da bunƙasa ilimi tare da horas da ƙwararru.

Fadar shugaban Nijar ta ce an cim ma matsaya kan aiwatar da ayyuka a waɗannan fannoni, inda Tiani ya buƙaci ɓangarorin biyu su hanzarta mayar da shirye-shiryen da aka tattauna zuwa ayyukan zahiri.

Ganawar na zuwa ne gabanin taron Rasha da Afirka da aka tsara gudanarwa a Moscow a ƙarshen watab Oktoban na wannan shekarar ta 2026.

Post a Comment

Previous Post Next Post