Majalisar dokokin jihar Kano, ita ma ta karɓi sabon ƙudirin dokar kafa ’yansandan jiha, inda ta fara nazari da duba tanaje-tanajen dokar domin ci gaba da tsarin kafa rundunar ’yansandan jihar.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai na kakakin majalisar jihar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar a ranar yau Juma’a, ya ce an rarraba kwafin ƙudirin takardun ga dukkan ’yan majalisar domin gudanar da cikakken nazari da bayar da shawarwari kan abubuwan da suke ganin ya dace a inganta.
Sanarwar ta bayyana cewa an riga an gabatar da ƙudirin a gaban majalisar yayin zamanta na baya, wanda ya bai wa ’yan majalisar damar fara nazari da la’akari da shi bisa tsarin dokokin majalisa.
Ana sa ran cewa bayan kammala nazarin da ’yan majalisar za su yi, za a gabatar da ƙudirin domin karatu na biyu a ranar 12 ga Oktoba, 2026, inda za a ci gaba da muhawara da duba tanaje-tanajensa.
Da yake magana kan matakin, Kakakin Majalisar Dokokin Kano, Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore, ya ce jihar Kano a shirye take ta tunkari ƙalubalen tsaro ta hanyar ɗaukar matakan da suka dace.
Falgore ya ce duk da cewa Kano na ci gaba da kasancewa cikin jihohin da ake samun zaman lafiya idan aka kwatanta da wasu sassan ƙasar, akwai buƙatar samar da dokokin da za su taimaka wajen ƙarfafa tsarin tsaron jihar.
Ya ƙara da cewa majalisar za ta ci gaba da tallafa wa duk wani mataki na doka da zai taimaka wajen inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.