L-PRES Ta Gabatar Da Rahoton Ci Gaba A Zamfara

Ofishin Gudanar da Ayyukan Shirin Tallafa wa Inganta Kiwo da Juriya (L-PRES) na Jihar Zamfara ya gabatar da rahoton ci gaban ayyukansa a yayin taron duba yadda ake aiwatar da shirin, wanda ke gudana a Yola, Jihar Adamawa.Ofishin L-PRES na Jihar Zamfara, ƙarƙashin jagorancin Mai Kula da Ayyukan Shirin na Jiha, Mohammed Nasiru, ne ya bayyana hakan a yammacin ranar Juma’a.

Tawagar Jihar Zamfara da ta halarci taron ta ƙunshi Mai Kula da Ayyukan Shirin na Jiha tare da manyan jami’an fasaha da na gudanarwa na shirin a jihar.

A cewar mai kula da shirin, an shirya taron ne domin duba ci gaban da aka samu wajen aiwatar da shirin, gano ƙalubalen da suka kunno kai, ƙarfafa haɗin gwiwa da kuma tabbatar da cimma manufofin shirin yadda ya kamata.

Ya bayyana cewa tattaunawar ta ba ofisoshin gudanar da shirin na jihohin da suka halarta damar musayar bayanai da tawagar masu sa ido kan yadda ake aiwatar da shirin, nasarorin da aka samu, ƙalubalen da ake fuskanta da kuma matakan da suka dace a ɗauka domin hanzarta ayyukan shirin.

A yayin zaman, Mai Kula da Ayyukan Shirin na Jihar Zamfara ya gabatar da rahoton ci gaban aiwatar da shirin a jihar, inda ya bayyana nasarorin da ofishin ya samu.

Nasarorin sun haɗa da gina da kuma gyara ababen more rayuwa da suka shafi kiwo, shirye-shiryen bunƙasa ƙwarewa da horas da waɗanda suka ci gajiyar shirin, tallafa wa manoman dabbobi da kayan aikin kiwo, gudanar da allurar rigakafin dabbobi a faɗin jihar, da kuma samar da wasu tallafe-tallafen fasaha ƙarƙashin shirin.

Tawagar Zamfara ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da ingantaccen aiwatar da shirin L-PRES a jihar, musamman wajen haɓaka yawan amfanin kiwo, ƙarfafa juriyar al’ummomin da suka dogara da kiwo da kuma bunƙasa kasuwancin kiwo mai ɗorewa.

A nasu jawaban, Jagoran Tawagar Masu Sa Ido Kan Shirin (TTL) da Mai Gudanar da Shirin a Ƙasa (NPC) sun yaba wa tawagar L-PRES ta Jihar Zamfara, musamman bisa ingancin ababen more rayuwa da aka samar ta hanyar shirin.

Post a Comment

Previous Post Next Post