PDP Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Cikakkun Bayanai Kan Shirin Rage Farashin Fetur na Kwanaki 30

Jam’iyyar PDP reshen Jihar Legas ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta bayyana cikakkun bayanai kan shirin da ta gabatar na rage farashin fetur na tsawon kwanaki 30, tare da neman a fayyace farashin ɗanyen mai, adadin rangwamen da za a bayar da kuma matakan da za a ɗauka domin ci gaba da tallafa wa masu amfani da fetur bayan kammala shirin.Jam’iyyar ta kuma nuna shakku kan shawarar sanya iyakar kuɗin da ake kashewa wajen samar da fetur a matakin tashar sauke mai ko kuɗin shigo da shi zuwa naira 1,350 kan kowace lita. Ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta bayyana yadda aka ƙididdige wannan adadi da kuma waɗanda za su ɗauki nauyin kuɗin shirin.

Kakakin jam’iyyar, Prince Christopher Odianarewo, ne ya yi wannan kira a ranar Alhamis, yayin da yake sukar matakan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sanar kan farashin man fetur.

Jam’iyyar ta ce sanarwar gwamnati cewa Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC Limited) zai sayar da fetur a farashin da ya saya na tsawon kwanaki 30, tare da shirin sayar da ɗanyen mai tun kafin lokacin samar da shi ga matatun mai na cikin gida, na buƙatar ƙarin bayani.

PDP ta buƙaci a bayyana ainihin adadin rangwamen da za a samu kan kowace lita, farashin da ake sayar da ɗanyen man Najeriya ga matatun mai na cikin gida da kuma ƙididdigar da aka yi amfani da ita wajen sanya iyakar naira 1,350.

Jam’iyyar ta kuma nemi Gwamnatin Tarayya ta bayyana matakan da za ta ɗauka domin kare masu amfani da fetur daga tsadar mai bayan kammala shirin na kwanaki 30.

Sanarwar ta ce: “PDP reshen Legas na buƙatar sanin ainihin adadin rangwamen, wanda zai ɗauki nauyin kuɗin da kuma abin da zai faru bayan kwanaki 30.”

Jam’iyyar adawar ta kuma yi tambaya kan dalilin da ya sa har yanzu ake danganta farashin man fetur ga farashin kasuwannin duniya da ake ƙididdigewa da dalar Amurka, tare da sauye-sauyen farashin canjin kuɗi, duk da cewa Najeriya na da ɗanyen mai da take samarwa a cikin gida da kuma matatun mai.

Ta bayyana cewa akwai buƙatar ƙarin bayani kan yadda ake ƙayyade farashin ɗanyen mai da ake samarwa a Najeriya da kuma kayayyakin man fetur da ake tacewa a cikin gida. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rahotannin da ke cewa matatar man Dangote ta rungumi tsarin ƙididdige farashin fetur bisa dala suka ƙara jawo damuwa kan tasirin sauye-sauyen farashin canjin kuɗi ga farashin mai a cikin gida.

Jam’iyyar ta ce bai kamata ’yan Najeriya su ci gaba da fuskantar tsarin farashi da ke danganta ƙarfin sayensu da ƙa’idojin farashin dala ba, ba tare da an yi cikakken bayani kan yadda ake ƙididdige kuɗaɗen samar da man ba.

Ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta fitar da ainihin farashin ɗanyen man Najeriya da ake sayar wa matatun mai na cikin gida, tare da bayyana yadda wannan farashi ke tasiri ga kuɗin da masu amfani da fetur ke biya.

A cewar jam’iyyar, abin da ’yan Najeriya ke buƙata shi ne sauƙin farashi mai ɗorewa, tsarin farashi na gaskiya da kuma riƙon amana, maimakon matakan wucin gadi waɗanda ba a fayyace tasirinsu ga kuɗaɗen gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki ba.

A ƙarshe, jam’iyyar ta buƙaci gwamnati ta bayyana waɗanda za su ɗauki nauyin rangwamen, ɓangarorin da za su amfana da shirin da kuma irin raguwar farashin da masu sayen fetur za su samu a gidajen mai.

Post a Comment

Previous Post Next Post