Tsoffin Masu Binciken AI uku Sun yi Gargaɗi Kan Illar Korarsu ga Al'adun Kamfanin

Tsoffin masu bincike uku sun wallafa wasiƙar gargadi , inda suka yi gargaɗin cewa korarsu  aiki na iya haifar da yanayin tsoro a tsakanin ma'aikatan kamfanin OpenAI, musamman waɗanda ke damuwa da haɗurran da ke tattare da fasahar basirar ɗan'adam ta wucin gadi (AI).An ce an kori masu binciken ne sakamakon ƙoƙarinsu na tabbatar da tsaron fasahar AI.

Masu binciken tsaron AI, Mikita Balesni, Tomek Korbak da Jasmine Wang, sun yi waɗannan zarge-zarge ne a ranar Alhamis, bayan da aka sallame su daga aiki a makon da ya gabata. Mutanen uku sun yi gargaɗin cewa matakin na iya hana sauran ma'aikatan da ke damuwa da haɗurran wannan fasaha ta zamani bayyana ra'ayoyinsu cikin 'yanci.

Sai dai OpenAI ta bayyana cewa ta sallame su ne saboda aikata laifukan da suka shafi rashin kulawa wajen sarrafa bayanan kamfanin.

Balesni ya bayyana a wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta na X cewa: “Na yi imanin cewa an kore mu ne saboda fifita tsaro fiye da muradun OpenAI na ɗan gajeren lokaci a matsayinta na kamfani.”

Shi ma Korbak ya bayyana irin wannan ra'ayi, inda ya ce yana ganin an sallame shi ne saboda ya nuna damuwarsa kan yadda OpenAI ke rasa ikon sa ido kan tunanin na'urorin AI masu gudanar da ayyuka da kansu. Ya ce wannan na daga cikin muhimman hanyoyin da ake amfani da su wajen gano lokacin da waɗannan na'urori suka aikata abin da bai dace ba.

A cikin wata wasiƙar buɗe ido da suka wallafa tare da saƙonninsu a shafukan sada zumunta, Balesni, Korbak da Wang sun bayyana damuwarsu cewa korarsu za ta sa tsoffin abokan aikinsu su ji tsoron yin magana ko aiki ta hanyoyin da, har zuwa makon da ya gabata, suke daga cikin muhimman al'adun aiki a OpenAI.

Sun ce: “Muna iya bayyana damuwarmu game da tsaro da kuma saɓa wa ra'ayin juna a fili, sannan ana ƙarfafa mu mu yi amfani da ƙwarewar ƙungiyoyin tsaro masu zaman kansu. Wannan na daga cikin abubuwan da suka bambanta OpenAI da sauran kamfanoni, kuma muna matuƙar alfahari da kasancewarmu cikin tawagar.”

Masu binciken uku sun ƙara da cewa idan mutanen da suka fi kusanci da haɗurran fasahar AI ba za su iya yin aiki tare cikin amana da musayar bayanai cikin sauƙi ba, tare da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyi na waje, to ba za a iya haɓaka wannan fasaha cikin aminci ba.

Sun ce: “Irin wannan al'adar aiki ce muke rubuta wannan wasiƙa domin karewa.”

A ƙarshe, mutanen ukun sun musanta karya ƙa'idojin kamfanin, inda suka bayyana cewa duk wata hulɗa da suka yi da ƙwararrun tsaro na waje ta dace da nauyin ayyukan da aka ɗora musu.

Post a Comment

Previous Post Next Post