Ɗanwasan ƙungiyar PSG ta Faransa da tawagar ƙasar Moroccco Achraf Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗanƙwallon kafa na Afirka na 2025.
Mohamed Salah na Masar da ƙungiyar Liverpool ne ya zo na biyu, sannan Victor Osimhen na tawagar Super Eagles ta Najeriya da ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya ya zo na uku.Hakimi ya samu nasarar lashe gasar cin kofin zakarun turai a ƙungiyar PSG ta kakar 2025, sannan ya lashe gasar Ligue 1 da Coupe de France da kuma UEFA Super Cup.