Rundunar sojin Amurka ta ce ta sake ƙwace wani jirgin ruwan dakon mai a yankin carribean, wanda ta ce ya saɓa abin da ta kira dokokin da Trump ya gindaya wa jiragen ruwa masu takunkumi.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, ya nuna yadda sojojin ruwa ɗauke da makamai ke tunkarar tankar mai suna Veronica, da kuma yadda suka shiga jirgin, a wani abu da suka kira samame na sanyin safiya wanda aka gudanar lami lafiya.Wannan ne jirgin ruwan dakon mai na shida da Amurka ta kama a baya bayan-nan, waɗanda ta ke zargi da dakon man Venezuela da aka sanya wa takunkumi.
Wata sanarwa da Amurkar ta fitar, ta ce babu man da zai fita daga Venezuela sai wanda aka sahale masa.