Yan Awaren Kudancin Yemen Sun Ki Janyewa Daga Jihohin Da Ke Kusa Da Saudiyya

 Majalisar Awaren Kudancin Yemen (STC) ta bayyana cewa ba za ta janye dakarunta daga wasu jihohi da ke arewacin kudancin Yemen, kusa da iyakar ƙasar Saudiyya, duk da matsin lamba da ake matsa mata daga ɓangarori daban-daban.

Kudancin Yemen

STC, wadda ke fafutukar kafa ƙasa mai zaman kanta a kudancin Yemen, ta ce kasancewar dakarunta a wadannan yankuna na da muhimmanci wajen kare tsaro da muradun al’ummar kudancin kasar, tana mai cewa ba za ta amince da duk wata yarjejeniya da za ta tauye ikonta ba.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Saudiyya da wasu ƙasashen yankin ke ƙoƙarin rage rikici a Yemen tare da karfafa zaman lafiya, musamman a yankunan da ke kusa da iyakokinsu. Rahotanni sun nuna cewa Riyadh na son ganin an rage yawan dakarun STC a wasu muhimman jihohi domin kauce wa tayar da sabon rikici.

Masu sharhi na ganin cewa kin janyewar STC na iya kara dagula al’amuran siyasa da tsaro a Yemen, tare da kawo cikas ga kokarin da ake yi na samar da cikakken zaman lafiya bayan shekaru da dama na yaƙi da rashin tabbas.

Duk da haka, STC ta jaddada cewa za ta ci gaba da tattaunawa, amma ba za ta amince da duk wani mataki da zai bar al’ummarta cikin barazana ko rage tasirinta a yankunan da take iko da su ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post