Gwamnatin Cuba ta bayyana cewa tana da cikakken haƙƙi na kare kanta da kuma martaba ƙasarta yayin da take fuskantar abin da ta kira ƙarin barazana da matsin lamba daga Amurka.
Jami’an gwamnatin Cuba sun ce ƙasar za ta ɗauki duk matakan da suka dace domin kare ikon mulkinta, tsaron ƙasa, da kuma ‘yancin tafiyar da harkokinta ba tare da katsalandan daga waje ba.
Wannan bayani na zuwa ne bayan wasu kalamai daga jami’an Amurka da suka soki gwamnatin Cuba kan batutuwan da suka shafi haƙƙin ɗan adam, takura wa ‘yan adawa, da kuma alaƙarta da wasu ƙasashen da Amurka ke ɗauka a matsayin abokan gaba.
Cuba ta zargi Amurka da ci gaba da aiwatar da tsohuwar manufar matsin tattalin arziki da katsalandan a harkokin cikin gidanta, ciki har da takunkuman tattalin arziki da Havana ta ce sun jefa tattalin arzikin ƙasar cikin matsala tare da shafar rayuwar al’umma.
Jami’an Havana sun jaddada cewa Cuba na ci gaba da goyon bayan zaman lafiya da diflomasiyya, amma ba za ta amince da duk wata barazana ga ikon ƙasarta ko harkokin cikin gidanta ba.
Dangantaka tsakanin Amurka da Cuba ta daɗe tana cikin tsami tun shekaru da dama, inda rikice-rikice kan siyasa, takunkumin tattalin arziki, ƙaura, da manufofin ƙetare suka ci gaba da haddasa rashin jituwar ƙasashen