APC Ta Sanya Gwamna Uba Sani Da Akpabio Don Jagorantar Yaƙin Neman Zaɓen Gwamnan Jihar Ekiti

ABUJA — Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanar da shirin ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe na Ƙasa domin fuskantar zaɓen gwamnan Jihar Ekiti. Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, shi ne aka zaɓa don ya jagoranci kwamitin, wanda aka ɗorawa alhakin tura gaba da kuma faɗaɗa harkokin kampe da tattara magoya baya gabanin gudanar da zaɓen.

Sakataren Yaada Labarai na Ƙasa na jam’iyyar APC, Felix Morka, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. Ya bayyana cewa za a ƙaddamar da Kwamitin Kampe na Ƙasa a ranar Laraba a birnin Abuja, inda Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, zai kasance mataimakin shugaban kwamitin (co-chairman).

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta riga ta tsaida ranar 20 ga watan Yuni, 2026 domin gudanar da zaɓen gwamnan na Jihar Ekiti.

Morka ya ƙara da cewa wannan ƙaddamarwa na nuna wani muhimmin mataki a yunƙurin jam’iyyar na fara gangamin neman zaɓe a fadin Jihar Ekiti gabanin babban zaɓen, da nufin samun gagarumar nasara a rumfunan zaɓe.

Sanarwar ta ƙunshi cewa: “Jam’iyyar All Progressives Congress za ta ƙaddamar da Kwamitin Kampe na Ƙasa a hukumance domin zaɓen Gwamnan Jihar Ekiti mai zuwa kamar haka:"

Post a Comment

Previous Post Next Post