Matatar Dangote Ta Dawo Da karbar Naira A Cinikin Mai

Matatar mai ta Dangote ta sake fara sayar da man fetur  da kuɗin naira bayan dakatarwar da ta yi na tsawon mako guda, tare da ƙara farashin fetur  zuwa N1,215 kan kowace lita, daga N1,075, wanda ya nuna ƙarin N140.

Matatar Man Dangote

An dakatar da sayar da fetur da naira ne bayan matatar ta koma amfani da dalar Amurka, inda ta danganta matakin da ƙarancin samun danyen mai a ƙarƙashin tsarin gwamnati na naira-for-crude.

Shugaban kungiyar masu gidajen mai masu zaman kansu (IPMAN), Alhaji Abubakar Maigandi, ya tabbatar da komawar tsarin naira, yana mai cewa hakan zai sauƙaƙa samar da fetur da kuma rage ƙarancin man da aka fuskanta a faɗin ƙasar a cikin makon da ya gabata.

Duk da ƙarin farashin, rahotanni sun nuna cewa fetur daga Matatar Dangote har yanzu ya fi na man da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje araha.

Post a Comment

Previous Post Next Post